<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ka Haƙura, Ya Raina, Haƙura LW331</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ka haƙura, ya raina, haƙura.
 Ubangiji kuwa yana wajenka,
 Ka haƙura, kome dai ya same ka,
 Azaba, sakewa, ko damuwa.
 Ga Allahnka zai shirya mafakatka,
 A ƙarƙashin fukafukansa kuwa.

[V2]
 2) Ka haƙura, ya rai na, haƙura.
 Sa'ad da taimako ya katse ma,
 Loton da abokai suka yashe ka,
 Babu dalili na yin fargaba.
 Ka dogara ga Allahnka kaɗai,
 Zai ƙarfafa zuciyarka sosai.

[V3]
 3) Ka haƙura, ya raina, haƙura.
 Masifa, mutuwa, ba ƙarshenmu ba.
 Ka tuna, ƴanuwanka duka fa,
 A hannun Yesu mai nasara ne.
 Da mu da su ma fita duhun nan,
 Ma shiga hasken Allahnmu a can.

[V4]
 4) Ka haƙura, ya raina, haƙura.
 Haƙuri maganin duniya ne.
 Talauci ne ko rashin lafiya,
 Ko damuwa ko kuwa hargitsi ne,
 A cikin Ruhun Allah ga murna,
 A cikin ƙaunar Yesu, ta'aziyya.</lyrics>
<hymn_number>331</hymn_number>
<author>Sibelius, Jean (1865-1957), von Schlegel, Katharina Amalia Dorothea (1697-1768)</author>
</song>